Masu zaman gudun hijra a sansanin Kuchingoro da ke birnin tarayya Abuja, sun koka da yadda gwamnati ta yi watsi da su kamar ba mutane ba.
Shugabar sansanin Philemon Emmanuel ta bayyana haka ne, yayin ziyarar da kungiyar tsofaffin daliban kwalejin ‘Kings ta kai masu a farkon wannan mako.
Philemon, ta ce su kan samu talklafi ne daga kungiyoyi masu zaman kan su amma ba daga gwamnati ba.
Idan dai ba a manta ba, a shekara ta 2014 ne, gwamnati ta kafa sansanin Kuchingoro domin sama wa ‘yan gudun hijira daga karamar hukumar Goza ta jihar Borno mafaka.
Sai dai bayan wani lokaci gwamnati ta sanar da mutane cewa su koma garuruwan su domin an ci karfin Boko Haram, amma da dama daga cikin su sun cigaba da zama a sansanin.
A cikin sansanin akwai rijiyar burtsatse dake amfani da hasken rana, asibiti daya, da makaranta daya wanda kungiyoyi masu zaman kan su da uwargidan tsohon ministan Abuja Bala Mohammed suka samar wa masu zama a sansanin.