Home Labaru Zaben Ekiti: Hukumar Zabe Ta Fitar Da Jerin Sunayen ‘Yan Takarar Kujerar...

Zaben Ekiti: Hukumar Zabe Ta Fitar Da Jerin Sunayen ‘Yan Takarar Kujerar Gwamna Na Karshe

374
0
Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamnan jihar Ekiti a zaɓen da za a yi ranar 18 ga watan Yuni na shekara ta 2022.

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamnan jihar Ekiti a zaɓen da za a yi ranar 18 ga watan Yuni na shekara ta 2022.

INEC, ta ce ta kafa sunayen ‘yan takarar ne a ofisoshin ta na jiha, da kuma kananan hukumomi a Ekiti da kafafen sada zumunta da doka ta amince da su.

Hukumar zaben, ta ce hakan ya yi daidai da abin da kundin dokokin zaɓe ya tanada, biyo bayan rufe karɓar ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa.

Wannan dai ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan hukumar zabe na ƙasa kuma shugaban kwamitin yada labarai Festus Okoye ya fitar.

Sanarwan ta nuna cewa, INEC ta amince da Abiodun Abayomi Oyebanji a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC da mataimakin sa Afuye Monisade, yayin da ta tantance Olabisi Kolawole a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP tare da Kolapo Olugbenga Kolade a matsayin mataimaki.

Leave a Reply