Wasu daga ciki manyan aminan siyasar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sun kai wa Sanata Ibrahim Shekarau ziyara a gidan sa dake Abuja.
Kakakin Sanata Shekarau Sule Ya’u ya tabbatar da ziyarar, inda aka tattauna a kan abubuwan da su ka shafi siyasar Jihar Kano.
Sai dai Sule Ya’u bai yi cikakken bayani akan abubuwa da aka tattauna a lokacin ziyarar ba, amma majiyoyi sun ce ta na da alaka da zawarcin Shekarau ya koma Jam’iyyar PDP.
Shekarau dai ya na fama da rikici a Jam’iyyar APC tsakanin shi da Gwamna Abdullahi Ganduje a kan jagorancin Jam’iyyar.