Home Labaru Sauyin Sheka: Abin Da Ya Sa Na Wancakalar Da Jam’iyyar Apc Samaila...

Sauyin Sheka: Abin Da Ya Sa Na Wancakalar Da Jam’iyyar Apc Samaila Suleiman

44
0
Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa Sama’ila Suleiman da aka fi sani da Farar Aniya ya fice daga jam’iyyar APC.

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa Sama’ila Suleiman da aka fi sani da Farar Aniya ya fice daga jam’iyyar APC.

A wata wasikar sanar da ficewar sa daga jam’iyyar, Sama’ila ya ce rikicin da ya dabaibaye APC a Abuja ne ya sa dole ya hakura da jam’iyyar.

ya ce wannan shawara da ya ɗauka ta zama dole, ganin yadda jam’iyyar APC ta shiga ruɗani da rarrabuwar kawuna, baya ga rashin sanin ainihin inda aka dosa, don haka ya ce daga yau ba shi ba jam’iyyar APC.

Wani jigo a jam’iyyar PDP ya shaida wa manema labarai cewa, da yiwuwar ɗan majalisar zai koma jam’iyyar PDP ne, domin har ya fara kwankwasa mata kofa ya na so ya tsunduma cikin ta ya nemi tikitin takara.

Sai dai wasu ‘yan jam’iyyar PDP sun ce abin da kamar wuya, domin tuni Shegu ABG ya na takarar kujerar a karkashin jam’iyyar kuma shi daɗaɗɗen ɗan jam’iyyar ne.