Home Labaru Zaben Bayelsa: Jam’iyyar APC Ta Zargi PDP Da Buga Katunan Zabe Na...

Zaben Bayelsa: Jam’iyyar APC Ta Zargi PDP Da Buga Katunan Zabe Na Bogi

363
0
Zaben Bayelsa: Jam’iyyar APC Ta Zargi PDP Da Buga Katunan Zabe Na Bogi
Zaben Bayelsa: Jam’iyyar APC Ta Zargi PDP Da Buga Katunan Zabe Na Bogi

Mataimakin babban sakataren jam’iyyar APC na kasa Yekini Nabena, ya yi zargin cewa jam’iyyar PDP ta fara buga katunan zabe na bogi gabannin zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Nabena ya yi zargin ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce jam’iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta sanya wa katin zaben na bogi suna ‘Biafra Card’ a Turance.

Ya ce katunan tantance masu zabe 22 kacal hukumar zabe ta yi nasarar kwatowa a cikin 69 da ‘yan bangar siyasa su ka sace a lokacin zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki na shekara ta 2019 a jihar.

Yakini Nabena, ya bukaci hukumar zabe ta tashi tsaye akan lamarin, sannan ta tabbatar ba a yi amfani da katin zabe na bogi a lokacin zaben ba.