Home Labaru Difilomasiyya: Ghana Ta Sake Rokon Nijeriya Ta Taimaka Ta Bude Iyakokin Ta

Difilomasiyya: Ghana Ta Sake Rokon Nijeriya Ta Taimaka Ta Bude Iyakokin Ta

268
0

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Ghana Mista Charles Owiredu, ya gana da karamin ministan harkokin wajen Nijeriya Ambasada Zubairu Dada, a kan ci-gaba da rufe iyakokin Nijeriya da kasashe makwafta.

Ganawar, ta biyo bayan ganawar da ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya yi da takwarar sa ta Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey da ministan kasuwanci na kasar Ghana Alan Kyerematen.

A ganawar, Ambasada Dada da Owiredu sun tattauna a kan hanyoyin kawar da kalubalen da ‘yan kasuwar Ghana da ke kokarin shigo da kaya Nijeriya ke fuskanta sakamakon kulle iyakokin ta.

Ambasada Dada ya tabbatarwa takwaran sa na Ghana cewa, Nijeriya ba ta yi hakan da nufin cutar da kasar Ghana ba, kawai ta na kokarin magance matsalolin da ta ke fuskanta ne a cikin gida.

Ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar rufe iyakokin ta ne na dan kankanin lokaci, saboda yadda ake fasa-kwaurin haramtattun kayayyki zuwa Nijeriya.