Home Labaru Nijeriya Da Saudiyya Sun Kulla Zumunci Na Kut-Da-Kut

Nijeriya Da Saudiyya Sun Kulla Zumunci Na Kut-Da-Kut

269
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi tayin bukatar kafa kakkarfar majalisa domin karfafa dankon zumuncin inganta hakokin kasuwanci da sauran huldodin diflomasiyya tsakanin kasashen Nijeriya da Saudiyya.

An dai cimma shawarar ne tsakanin Buhari Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman da Shugaba Buhari, matsayin daya daga cikin manyan muhimman batutuwan da shugabannin biyu su ka tattauna.

Kasashen biyu dai na cikin sahun gaba na manyan kasashe masu arzikin man fetur a fadin duniya, inda kasar Saudiyya ta kasance ta farko yayin Nijeriya ke matsayi na bakwai.

Da farko an shirya gudanar da taro tsakanin shugabannin kasashen biyu a fadar Yarima Salman, amma daga baya saboda girmamawa, sai Salman ya zabi ya yi tattaki ya samu Buhari har babban dakin da aka saukar da shi a shahararren Otal na Riyadh mai suna Riz Charlton Hotel.

Salman da Buhari sun amince da cewa, za a zabi manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa da masana tattalin arziki daga kasashen biyu su kasance ‘yan majalisar.