Home Labaru Zaben Bayelsa: APC Za Ta Iya Kada PDP- Goodluck Jonathan

Zaben Bayelsa: APC Za Ta Iya Kada PDP- Goodluck Jonathan

559
0
APC-VS-PDP
APC-VS-PDP

Tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya ce idan ba a samu hadin kai a jam’iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ba akwai yiwuwar jam’iyyar APC za ta kayar da PDP a zaben gwamnan jihar da za a yi a watan Nuwamban 2019.

Goodluck Jonathan, Tsohon Shugaban Kasa

Mai ba da shawara na musamman ga gwamna Seriake Dickson kan kafafen watsa labarai, Fidelis Soriwei, ya ce tsohon shugaban kasan ya fadi haka ne yayin taron kwamitin dattawan PDP da aka yi a gida gwamnati da ke Yenagoa.

Jonathan ya ce hadin kai ne kawai zai iya ba jam’iyyar PDP nasara idan bah aka ba jam’iyyar APC za ta iya lashe zaben.

Karanta Wannan: Lakabi: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Fitar Da Sabon Hoto Da Suna A Hukumance

Ya ce duk da cewa jam’iyyar APC a jihar Bayelsa ba ta da wani karfi a matakin mazabun kananan hukumomi da jihar, sai dai za ta iya lashe zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamban 2019,  dan haka ya zama wajibi PDP ta hada kai domin samun nasara.

Ya ce matukar suna son jam’iyyar PDP ta yi nasara a jihar, suna bukatar hada kai dan haka ya zama dole ‘yan takaran PDP 21 su hada kan su a karshe A yi wa duk wanda ya zama dan takarar aiki.