Home Labaru Kotu Ta Ba EFCC Damar Kulle Asusun Tsohon Gwamnan Legas

Kotu Ta Ba EFCC Damar Kulle Asusun Tsohon Gwamnan Legas

205
0

Hukumar hana zambar kudi da karya tattalin arzikin kasa EFCC ta ce ta bankado tare da sanya wa wasu asusun banki guda uku takunkumi wadanda ke dauke da zunzurutun kudi sama da Naira miliyan 9 wadanda ke da nasaba da tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode.

Tony Orilade, mai magana da yawun EFCC.
Tony Orilade, mai magana da yawun EFCC.

Hukumar EFCCn, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta, Tony Orilade, ya fitar ta ba da umarnin sanya takunkumi kan asusun kan zargin badakalar.

Orilade ya bayyana cewa, mai shari’a Chuka Obiozor, dake Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas, ya ba da umarnin sanya takunkumin.

Asusun ajiyar sun hada da na bankin First City Monument, da bankin Access, da kuma bankin Zenith.

Mai shari’a Chuka Obiozor, ya ba da umarnin ne, bayan wani korafi da Hukumar EFCC ta shigar gaban sa na neman  kotun ta sanya wa asusun takunkumi har zuwa sanda hukumar zata kammala bincike.