Home Labaru Nasara: Ganduje Ya Ba ’Yan Wasan Kano Pillars Dala Dubu Dai-Dai

Nasara: Ganduje Ya Ba ’Yan Wasan Kano Pillars Dala Dubu Dai-Dai

636
0
Ganduje Ya Ba ’Yan Wasan Kano Pillars Dala Dubu Dai-Dai
Ganduje Ya Ba ’Yan Wasan Kano Pillars Dala Dubu Dai-Dai

Daukacin ‘yan wasan Kano Pillars da Shugabannin su, sun samu kyautar Dala dubu guda-guda daga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Hakan na cikin wani bangare na alhairin da ake sa ran gwamnan zai yi wa ‘yan wasan kafin kuma gagarumar walimar da a ke shirin shirya wa nan ba da jimawa ba.

Karanta Wannan: Mu Daina Zargin Kowa Game Da Matsalar Tsaro A Nijeriya – Obasanjo

Gwamna Umar Ganduje, ya ce domin nuna farin cikin nasarar da ‘yan wasan suka samu, yana mikawa ‘yan wasan da kuma Shugabannin Kungiyar ta Kano Pillars wanda adadin su yan kai 40, wannan kyauta da daya ne daga cikin sauran kyaututtukan da za su biyo baya nan da dan lokaci kadan.

Gwamnan na yin wannan jawabi ne, a lokacin da tawagar Kungiyar Kano Pillars ta ziyar ce shi a Fadar Gwamnatin ta Kano, domin isar da godiyar su tare da gabatar da Kofin da suka samu nasarar lashewa ga Gwamnan.

Da ya ke tsokaci kan karawar da aka yi, wanda a karshen al’amarin nasara ta samu ga Kano Pillars, gwamna Ganduje, ya tabbatar musu da ci gaba da samun goyon bayan sa tare da jajircewa wajen ciyar da kungiyar gaba da kuma sauran bangarorin wasanni a Jihar Kano.

Kungiyar Kano Pillars dai ta doke kungiyar Niger Tornados, ne a wasan karshe na gasar cin kofin kalubale na kasa wanda ta kwashe shekara 60 rabon da ta lashe kofin.