Home Labaru Siyasa Zaben 2023: Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinonin Zabe

Zaben 2023: Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinonin Zabe

13
0
PRESIDENT BUHARI PRESIDES OVER FEC MEETING/SWEARS IN 3-NEW INEC NATIONAL COMMISSIONERS 5B. President Muhammmadu Buhari, Vice President Yemi Osinbajo SAN, SGF Mr Boss Mustapha, Minister of Justice Abubakar Malami SAN AS three new INEC Commissioners; Dr. Baba Bila, Prof Abdullahi Abdu Zuru and Prof Sani Mohammad Adam (SAN) takes oaths during their swearing-in before the FEC Meeting held at the State House, Abuja. PHOTO; SUNDAY AGHAEZE. SEPT 15TH 2021.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da kwamishinonin hukumar zabe na kasa guda 3, inda ya bukaci su jajirce wajen bada gudumawar tabbatar da zabe mai inganci a Nijeriya.

Kwamishinonin kuwa su na daga cikin wadanda Majalisar Dattawa ta amince da nadin su a watannin da su ka gabata.

Daga cikin su akwai Farfesa Muhammad Sani Adam, da Dr Baba Bila da kuma Farfesa Abdullahi Abdul.

Bikin rantsuwar ya gudana ne gabanin taron majalisar zartarwa ta kasa da aka saba gudanarwa kowace ranar Laraba a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ana saran sabbin kwamishinonin za su bada gudumawa wajen shirin zaben shekara ta 2023.