Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da kwamishinonin hukumar zabe na kasa guda 3, inda ya bukaci su jajirce wajen bada gudumawar tabbatar da zabe mai inganci a Nijeriya.
Kwamishinonin kuwa su na daga cikin wadanda Majalisar Dattawa ta amince da nadin su a watannin da su ka gabata.
Daga cikin su akwai Farfesa Muhammad Sani Adam, da Dr Baba Bila da kuma Farfesa Abdullahi Abdul.
Bikin rantsuwar ya gudana ne gabanin taron majalisar zartarwa ta kasa da aka saba gudanarwa kowace ranar Laraba a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ana saran sabbin kwamishinonin za su bada gudumawa wajen shirin zaben shekara ta 2023.

