Home Labaru Tsaro: Buhari Na So A Yi Doka A Kan Shigo Da Makamai...

Tsaro: Buhari Na So A Yi Doka A Kan Shigo Da Makamai Da Ababen Fashewa Nijeriya

13
0
Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dattawa bukatar yin dokar da za ta sa ido a kan shigo da kananan makamai, da kuma saye da saida abubuwan fashewa a Nijeriya.

Kudurorin biyu dai sun hada da sa ido a kan kananan makamai da kuma ababen fashewa.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ya karanto wasikar da ke kunshe da kudurorin a zaman majalisar na ranar Talatar da ta gabata.

A cikin wasikar, Shugaba Buhari ya ce ‘akwai bukatar sa ido a kan yadda ake samarwa da ajiyewa da mallaka da amfani da rabawa da saye da kuma saida ababen fashewa.’

Wasikar, ta kuma bukaci a maida kwamitin Shugaban Kasa a kan Kananan Makamai zuwa Cibiyar Lura da Kananan Makamai ta Kasa, wadda za ta yi aiki a karkashin ofishin mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro.