Home Labaru Cike Gurbi: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Rantsar Da Sabon Sanatan Jam’iyyar PDP

Cike Gurbi: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Rantsar Da Sabon Sanatan Jam’iyyar PDP

23
0

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya rantsar da sabon dan majalisar dattawa na jam’iyyar PDP, Agom Jarigbe, wanda zai maye gurbin Stephen Odey kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Jarigbe dai ya jima su na fafatawa a shari’a da Steven Odey, a kan halastaccen ɗan takarar da jam’iyya ta tsaida a zaɓen cike gurbi na kujerar sanata mai wakiltar mazabar Cross Rivers ta arewa.

Agom Jarigbe, ya karbi rantsuwar kama aiki daga shugaban majalisar ne bayan samun nasara a kotun ƙoli.

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa dai ta gudanar da zaɓen cike gurbi na mazaɓar Cross Rivers ta arewa ne bayan mutuwar sanata Rose Oko.