Home Home Za A Fuskanci Ambaliyar Ruwa A Daminar Bana A Najeriya – NEMA

Za A Fuskanci Ambaliyar Ruwa A Daminar Bana A Najeriya – NEMA

29
0
Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa NEMA, ta ce za a fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a daminar shekara ta 2023.

Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa NEMA, ta ce za a fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a daminar shekara ta 2023.

Shugaban hukumar Mustapha Ahmed ya bayyana haka, lokacin wani taro da hukumar ta shirya a Abuja.

Duk da dai hukumar ba ta fayyace wuraren da ambaliyar za ta fi shafa ba, amma ta ce shiryawa da wuri zai taimaka wajen rage ɓarnar da za ta iya haifarwa.

A daminar da ta gabata dai, an samu mummunar ambaliya a yankunan Nijeriya daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dukiya mai ɗimbin yawa.

Mustapha Ahmed, ya ce babu ko shakka za a samu ambaliyar ruwa a wannann shekarar, kuma ba su san irin ɓarnar da za ta yi ba.