Wata kungiyar siyasa da ta ke neman jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023, ta samu masoya miliyan guda a halin yanzu.
Rahotonni sun ce ana hurowa tsohon gwamnan Legas wuta ya nemi takara domin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Duk da wannan kururuwa da ake ta yi, har yanzu tsohon gwamnan bai yanke hukuncin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba, ganin cewa akwai sauran lokaci tukuna.
Bola Tinubu, ya taba bayyana cewa abinda ke gabansa a yanzu shi ne yadda zai ba gwamnatin shugaban kasa Buhari shawarwarin yadda za ta kai ga nasara, ba siyasar 2023 ba.
Kungiyar mai suna Tinubu 2023, Not Negotiable wanda aka fi sani da TNN, ta yi bikin cika shekara guda kwanan nan, ta kuma bayyana cewa ta na kara samun magoya baya har a kasashen waje.
Wani tsohon jigon PDP wanda yanzu ya koma tafiyar APC, Mutiu Okunola, ya ce a 2023, babu abinda zai hana Bola Tinubu za ma shugaban kasa, saboda ya cancanci ya rike Najeriya, domin shi kadai ne zai iya kai Najeriya ga ci idan ya samu mulki.
You must log in to post a comment.