Home Labaru Kwarewar Aiki: Buhari Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Hukumar Tsaro Ta Civil Defence

Kwarewar Aiki: Buhari Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Hukumar Tsaro Ta Civil Defence

95
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita wa’adin kwamandan rundunar tsaro ta Civil-Defence  a Najeriya Abdullahi Gana Muhammadu.

Shugaban kasa ya amince a tsawaita wa’adin shugaban hukumar daga yanzu har zuwa tsawon watanni shida. Mai magana da yawun kwamanda Janar Gana, Ekunola Gbenga, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sabanin rade-radin da ke yaduwa na cewa Buhari ya sabunta nadin kwamandan rundunar na tsawon shekaru biyar da zai kare a ranar 17 ga watan Yulin 2020, ya ce labarin kanzon kurege ne.

Gbenga, ya ce wannan zantuttuka ne kawai na shaci fadi da wasu ke kirkira domin su haifar da matsala a hukumar.

Ya ce Buhari ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar ne ta hannun Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, kuma za ta fara aiki ne daga ranar 17 ga watan Yulin 2020.

An tsawaita wa’adin Kwamandan ne bisa la’akari da kwazon aiki da kuma rawar da ya taka wajen bunkasa harkokin gudanarwa da kuma inganci a hukumar.