Ofishin hukumar shige da fice da ke Katsina ya karbi ‘Yan Nijeriyan su 42 da aka dawo da su daga Nijer ta mashigin Kongolam, sakamakon shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
Mutanen masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 sun bi ta barauniyar hanya ce suka shiga kasar ta Nijer domin kauce wa tantancewar hukumar shige da fice.
Ba da jimawa ba dai ana sa ran za a gurfanar da ragowar 30 din da suka rage bayan kammala binciken laifin da suka aikata.
Da yake magana kan lamarin, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa Muhammad Babandede, ya bayar da umurnin a gaggauta gurfanar da ragowar da suka rage ba tare da wani bata lokaci ba.
A hukuncin da mai shari’a Hadiza Shagari ta yanke, ta wajabta wa wadanda ake tuhuma ko su biya tarar Naira dubu 50 ko kuma a daure su a gidan gyaran hali na tsawon wata uku.