Home Labaru Zaben 2019: Shugaba Buhari Ya Maida Martani A Kan Rahoton Tarayyar Turai

Zaben 2019: Shugaba Buhari Ya Maida Martani A Kan Rahoton Tarayyar Turai

482
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta na maraba da rahoton da Tarayyar Turai ta fitar a kan zaben shekara ta 2019.

Mai magana da yawun Shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana haka a wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Ya ce gwamnati ta yi alkawarin duba rahoton dalla-dalla, sannan za ta yi aiki da shawarwarin da rahoton ya kunsa.

Garba Shehu, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta jajirce wajen tabbatar da tsarin damokradiyya mai tsafta, shi ya sa ta goyi bayan gayyatar da hukumar zabe ta yi wa masu sa ido na Tarayyar Turai.

Ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa an gyara duk wasu kura-kurai a zabe na gaba, ta hanyar hada kai da duk ‘yan Nijeriya da hukumomi da jam’iyyu da kungiyoyin farar hula da kafofin yada labarai da sauran masana, wajen ganin an gyara nakasun da ke tattare da tsarin zaben Nijeriyar kamar yadda Tarayyar Turai ta bayyana.

Garba Shehu, ya ce gwamnati ta yi takaicin tashe-tashen hankula da aka yi a wasu bangarorin kasar nan kamar yadda rahoton Tarayyar Turai ya nuna, sai dai gwamnati ba ta ganin rikice-rikicen sun yi tasiri a sakamakon zaben.