Home Labaru Difilomasiyya: Nijeriya Na Neman Bahasi A Kan Kisan Al’ummar Ta A Afrika...

Difilomasiyya: Nijeriya Na Neman Bahasi A Kan Kisan Al’ummar Ta A Afrika Ta Kudu

446
0
Gwamnatin Tarayya

Shugaban Ofishin jakadancin Nijeriya a kasar Afrika ta kudu Mr Godwin Adama, ya ce Ofishin ya shirya domin fara neman bahasi daga jami’an tsaron Johannesburge, a kan yadda ake gallazawa, tare da kisan ‘yan Nijeriya a kasar ba tare da daukar mataki ba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriyar ya ruwaito Godwin Adama na cewa, daukar manyan matakai ya zama wajibi, duba da yadda lamarin ke kara tsananta, bayan kisan ‘yan Nijeriya 130 a cikin watanni 30, wanda ya ce adadin na ci-gaba da karuwa a kowane lokaci.

Idan dai ba a manta ba, a watannin baya shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa takwaran sa Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudun korafi a kan yadda ake yi wa ‘yan Nijeriyar Kisan gilla.

Leave a Reply