Ana kyautata zaton tsohon gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode zai samu gurbin minista daga jihar Legas a cikin majalisar da shugaba Muhammadu Buhari zai kafa.
Kwamitin amintattu na jam’iyyar APC ne ya ba shugaban kasa shawarar bada mukamin minista ga duk gwamnonin jam’iyyar da ba su samu komawa a zango na biyu ba.
Bisa wannan shawara ta uwar jam’yyar APC ne, ake kyautata zaton Ambode da tsohon gwamnan jihar Adamawa Mohammed Bindow da tsohon gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar za su samu mukamin minista.
Sai dai Ambode ya na fuskantar gagarumin kalubale daga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da su ka hana shi samun tikitin takarar gwamna a karo na biyu.
Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC a jihar Adamawa Ahmed Lawan, ya ce mai yiwuwa Bindow ya samu mukamin minister, kamar yadda wata majiya ta tabbatar da cewa, masu ido da kwalli a fadar shugaban kasa sun ce Ambode zai iya samun mukamin minista duk da ya gaza cin zaben cikin gida na jam’iyyar APC a jihar Legas.