Home Labaru Zabe: An Soma Kada Kuri’a A Kasar Guinee Bissau

Zabe: An Soma Kada Kuri’a A Kasar Guinee Bissau

334
0
Zabe: An Soma Kada Kuri’a A Kasar Guinee Bissau
Zabe: An Soma Kada Kuri’a A Kasar Guinee Bissau

A ranar Lahadin nan ne, ‘yan kasar Guinee Bisseau su ka soma kada kuri’u zagaye na biyu a zaben Shugaban kasar da zai hada tsofin Firayin ministocin kasar da su ka hada da Domingos Simoes Pereira, wanda ya samu kashi 40 da ‘yan kai na kuri’u da abokin takarrar sa Ummar Sissoco Embalo da ake kallo a matsayin wanda ke da manufofin da su ka sha bamban da na gwamnatin kasar.

Kasar Guinee Bissau dai ta yi kaurin suna wajen juyin mulki ne, biyo bayan rashin jituwa tsakanin ‘yan siyasa.

Cimma wannan matsaya da ya kai ‘yan siyasa amincewa da kudurorin da aka cimmawa bayan tsawon lokaci ana tattaunawa da kungiyar Ecowas ne ya taimaka wajen shirya wannan zabe.

Yanzu haka sojojin kasar sun dauki alkawarin nisanta kan su daga duk wani zance da ya shafi siyasa.

Hukumar zaben kasar ta bayyana yawan masu kada kuri’a da akalla dubu 700 da su ka karbi katunan zabe.