Tsohon Madugun ‘yan Tawayen Cote D’Ivoire kuma tsohon Shugaban Majalisar kasar Guillaume Soro da hukumomin kasar ke nema ruwa a jalo, ya ce babu tanttama zai shirya gwagwarmaya domin kawar da Shugaban kasar Alassane Dramane Ouattara daga Faransa.
Guillaume Soro, ya ce tabbas zai tsaya takara a zaben shugabancin Cote D’Ivoire a matsayin jarumi, tare da yin koyi da Janar De Gaulle, mutumin da a wancan lokaci daga London ya kadammar da wani shirin kwato Faransa daga hannun makiya.
Soro dai ya fuskanci fushin hukumomin Cote D’Ivoire da su ka haramta ma shi shiga kasar a lokacin da ya dawo daga balaguro, lamarin da ya tislasa wa jirgin da ke dauke da shi sauka a kasar Ghana kafin daga bisani ya kama hanyar zuwa Turai.
Soro ya bayyana aniyar shi ta tsayawa takarar ne, a cikin wata hirar hadin gwiwa da ta hada shi da kafafen yada labarai na kasar Faransa,
Kimanin shekaru 2 da su ka gabata ne, aka samu baraka tsakanin Soro da shugaba Alassane Ouattara, wanda ake ganin ya na kokarin sake yin wa’adi na 3 a jere.
You must log in to post a comment.