Home Home Za Mu Ɗauki Ma’aikata Miliyan 1.4 Don Gudanar Da Aikin Zaɓe –...

Za Mu Ɗauki Ma’aikata Miliyan 1.4 Don Gudanar Da Aikin Zaɓe – INEC

32
0
Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce za ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi kimanin miliyan 1 da dubu 400 a zaben shekara ta 2023.

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce za ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi kimanin miliyan 1 da dubu 400 a zaben shekara ta 2023.

Ma’aikatan da hukumar za ta dauka kuwa sun hada da masu yi wa ƙasa hidima da ɗaliban manyan makarantu da ke shekarar ƙarshe domin taimaka mata gudanar da aikin zaɓen da ke tafe.

Babban kwamishina kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri’a na hukumar Festus Okoye ya bayyana haka, a cikin shirin ‘Morning Show’ na gidan Talbijin na Arise.

Hukumar zaben, ta akuma gargaɗi masu sayen ƙuri’un mutane da masu ƙirƙirar lambobin katin zaɓe su daina aikata hakan, domin a cewar sa, akwai bayanan kowane kati a kan na’urar tantance masu kaɗa lkuri’a, don haka sayen kuri’a ba zai amfanar da su da komai ba.

Festus Okoye ya ƙara da cewa, ‘mun bayyana ƙarara cewa hukumar zabe za ta kai na’aurar tantance masu kaɗa kuri’a a rumfunan zaɓe domin tantance masu zaɓe, kuma bayanan kowa su na ƙunshe a cikin na’urar maimakon jikin katin zaɓen.