Home Home Jam’iyyun APC Da PDP Sun Yi Martani Kan Goyon Bayan Obasanjo Ga...

Jam’iyyun APC Da PDP Sun Yi Martani Kan Goyon Bayan Obasanjo Ga Peter Obi

29
0

Jam’iyyun APC daa PDP, sun maida wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo martani, game da ikirarin da ya yi cewa matasan Nijeriya su goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar Labour Peter Obi.

Babban daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jam’iyyar APC Bala Ibrahim, ya ce maganar Obasanjon ba wani abin damuwa ba ne domin ba wata magana ce sabuwa ba.

Ya ce ba ya so ya ƙaskantar da matsayin Obasanjo da martabar sa da darajar sa a matsayin sa na tsohon shugaban ƙasa, amma gaskiyar magana ita ce ya zama mushen gizaka, yara kawai ya ke ba tsoro babu wani tasiri a abubuwan da ya ke.

Ya ƙara da cewa Obasanjo ko akwatinsa ma baya kawowa, ballantana ƙasa ba ki ɗaya. Sannan kuma ya ce dama Obasanjon ya saba da irin wannan kira a baya kuma kiran nasa baya wani tasiri.

A bangaren jam’iyyar PDP kuma, daya daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar Sanata Ibrahim Tsauri, ya ce tsohon shugaban ƙasar ya na fama da gigin tsufa ne, domin yanzu idan ya yi maganganu ba a ɗaukar su a matsayin kura-kurai, saboda idan ya furta magana daga baya ba zai iya maimaita abin da ya faɗa ba.