Home Home Maganar Rashin Lafiyata Shirme Ne Kawai – Tinubu

Maganar Rashin Lafiyata Shirme Ne Kawai – Tinubu

37
0
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana zancen rashin lafiyar sa da ake yayatawa a matsayin tsohon labari kuma shirme.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana zancen rashin lafiyar sa da ake yayatawa a matsayin tsohon labari kuma shirme.

Tinubu ya bayyana haka ne, yayin gudanar da aikin Umara a kasar Saudiya, inda ya ce ya kammala sassarfa tsakanin dutsunan Safa da Marwa har sau bakwai, wanda mutum maras koshin lafiya ba zai iya yi ba.

Masu sukar Tinubu dai na ci-gaba da cewa ba zai iya shugabantar Nijeriya ba bisa dalilai na rashin cikakkiyar lafiya.

Wannan dai ya na zuwa ne, a daidai lokacin da ya rage ‘yan makonni kadan a gudanar da zaben shugaban kasa, inda Tinubu zai fafata da manyan ‘yan takara irin su Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi.