Home Featured Za a ba da sakamakon gwajin COVID-19 1,000 kullum a Najeriya

Za a ba da sakamakon gwajin COVID-19 1,000 kullum a Najeriya

739
0

Akalla mutum 2,000 ne aka yi wa gwajin cutar coronavirus a Najeriya kawo yanzu. Nan ba da jimawa ba kuma za a rika yi wa mutum 500 zuwa 1,000 gwajin cutar a kullum.

A jawabinsa ga taron Kwamitin Aiki da Cikawa na Shugaban Kasa kan Yaki da Cutar Coronavirus, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce an samu karin cibiyoyin gwajin cutar guda biyu.

Ma’aikatar Lafiyar Najeriya ta ce kashi 70 na masu cutar coronavirus a maza ne, sauran kashi 30 din kuma mata ne.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya ce yawancin mazan da suka kamu da cutar coronavirus a kasar ‘yan shekara 30 zuwa 60 ne.

Ya kara da cewa duk da haka, maza da mata masu kowane irin shekaru na iya kamuwa da cutar.

Da yake bayar da alkaluman cutar, Ehanire ya ce gwamnati na kokarin kara yawan cibiyoyin gwajin cutar da kuma fitar da sakamakon gwajin da sauri a fadin kasar.

Ministan ya ce nan ba da jimawa ba, za a rika fitar da sakamakon gwajin cutar coronavirus guda 500 zuwa 1,000 a kowace rana.

Ya kuma ce mutum 2 cutar ta kashe a kasar na fama da wasu cututtuka masu tsanani tun kafin su kamu da coronavirus.

A cewarsa, kamuwarsu da COVID-19 ta kara tsananta cututtukan da ke damun mutanen, har ta yi ajalinsu.

Kawo yanzu mutum 174 suka kamu da cutar a kasar, bayan an samu karin mutum 23 a ranar Laraba 1 ga Afrilu, 2020.