Home Labaru Kiwon Lafiya Mutum na 4 ya harbu da coronavirus a Kaduna

Mutum na 4 ya harbu da coronavirus a Kaduna

945
0
El-Rufai Ya Bada Umurni Rufe Shagunan Saida Gas A Cikin Unguwanni
El-Rufai Ya Bada Umurni Rufe Shagunan Saida Gas A Cikin Unguwanni
El-Rufai Ya Bada Umurni Rufe Shagunan Saida Gas A Cikin Unguwanni
Gwamna Nasir El-Rufai shi ne wanda ya fara kamuwa da cutar coronavirus a Jihar Kaduna

Hukumomi sun tabbatar da kamuwar mutum na 4 da cutar coronavirus a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kamishinar Lafiyar Jihar Kaduna, Hadiza Mohammed Baloni ta sanar da hakan a cikin wani sako da ta fitar.

Samun karin wanda cutar coronavirus ta kama a jihar na zuwa ne a ranar da gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita da ta sanya, domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Ma’aikatar Lafiyar jihar ta ce tana kokarin gano mutanen da masu cutar suka yi hulda da su domin a killace, a kuma lura da su.

Ta kara da cewa dukkan masu cutar a jihar na samun kulawar da ta dace yayin da ake kokarin bibiya da kuma gano abokan huldarsu.

Sanarwar ta kuma bukaci jama’ar jihar da su rika bin matakan tsafta, musamman na wanke hannu akai-aikai, da nisantar kusantar juna sosai, domin takaita yaduwar cutar.

Gwamnan jihar, Nasir El-rufa’i shi ne mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar, kuma tuni ya killace kansa.