Home Labaru Kiwon Lafiya Mutumin Da Ya Fara Kamuwa Da COVID-19 Ya Warke

Mutumin Da Ya Fara Kamuwa Da COVID-19 Ya Warke

390
0
Mutumin da ya fara kamuwa da COVID-19 ya warke.
Mutumin da ya fara kamuwa da COVID-19 ya warke.

Mutumin da ya fara kamuwa da cutar coronavirus ya warke, har an sallame shi daga asibiti a Jihar Oyo da ke Kudu maso yammacin Najeriya.

Gwamantin jihar oyo ta tabbatar da sallamar mara lafiyan daga asibitin da ake killace shi.

Sanarwar hakan na zuwa ne washegarin ranar da gwamnatin jiahr ta sanrar da cewar gwamnan jihar Seyi Makinde, kamu da cutar coronavirus.

Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin ‘yan jarida, Taiwo Adisa, ya ce an gano mutumin na dauke da cutar coronavirus ne bayan an yi masa gwajin cutar sau biyu.

Ya ce gwajin farkon da aka yi wa mutumin bayan dawowarsa daga kasar Amurka ya nuna bai kamu da cutar ba, amma a karo na biyu sai sakamakon gwajin ya nuna yana dauke da kwayar cutar.

Ya kara da cewa, sai da aka yi wa mutumin gwaje-gwaje, kuma sau biyu a jere sakamakon gwajin na nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar, kafin aka sallame shi daga inda aka killace shi na tsawon kwana shida.

Sanarwar ta kuma kara da cewa likitoci za su ci gaba da lura da yanayin mutum a tsawon lokaci.