Home Labarai Yunƙurin Hana Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomin Kano: Kotu Ta Dakatar Da CBN

Yunƙurin Hana Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomin Kano: Kotu Ta Dakatar Da CBN

244
0
courtss 688508 772421 850x460
courtss 688508 772421 850x460

Wata babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin hana hukumomin tarayya dakile kason kudaden da ake ba kananan hukumomi 44 na jihar duk wata.

Rahotanni na cewa, hukuncin kotun ya biyo bayan karar da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE) da sauran mazauna jihar suka shigar a gaban kotun a ranar 1 ga Nuwamba, 2024.

A cikin umarnin mai dauke da kwanan watan 4 ga watan Nuwamba, Mai shari’a Muhammad ya ba masu shigar da kara izinin mika takardun umarnin kotun.

Ga ofishin Akanta Janar na Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar tsimi da tanadi kan tattara haraji na kasa (RMAFC).

Karar wacce aka shigar, ta nuna damuwa kan yiwuwar hanawa ko kuma jinkirin fitar da kudaden da ake ba kananan hukumomi a jihar.

An dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga Nuwamba, 2024.

Leave a Reply