Home Muryar 'Yanci Gwamnatin Najeriya Ta Kwace Kwangilar Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Gwamnatin Najeriya Ta Kwace Kwangilar Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

205
0
Julius Berger 1000x600
Julius Berger 1000x600

Gwamtain tarayya ta sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar gina hanyar Abuja zuwa Kaduna da ta ƙulla da kamfanin Julius Berger.

Bayan cikar wa’adin kwana 14 da gwamnatin ta ba kamfanin na ɗaukar mataki kan tafiyar Hawainiya da aikin ke yi, a yanzu ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar ba tare da samun damar yin wata tattaunawa ba.

Baya ga  tafiyar Hawainiya da aikin ke yi, ana kuma zargin sa da ƙin bada cikakken bayani kan kuɗin da aikin ya laƙume kawo yanzu, da ƙin biyayya ga dokokin da aka shimfida, da kuma ƙin biyayya ga shawarwarin da ma’aikatar ayyuka ta bashi.

An dai shafe tsahon watanni ana yamutsa gashin baki tsakanin kamfani da gwamnati kan waɗannan matsaloli da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.

Ta cikin sanarwar da ma’aikatar ayyukan ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta Mohammed Ahmed, ta ce an shafe wata 13 a jere ana tattaunawa da kamfanin amma an kasa cimma matsaya, domin haka babu wani zabi da ya wuce kawo ƙarshen yarjejeniyar.

Leave a Reply