Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 a Nasarawa

‘Yan Sanda Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 a Nasarawa

1
0

Jami’an ‘Yan sanda sun kashe wasu mutane uku da ake zargin
‘yan bindiga ne a Karamar Hukumar Lafiya ta Jihar
Nasarawa.

An dai kashe wadanda ake zargin ne yayin wani artabu da su
ka yi da jami’an ‘yan sandan, inda aka cewa ceto wani mutum
da su ka sace mai suna Ezekiel Luka daga Jihar Taraba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ramhan Nansel ya
bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce
jami’an ‘yan sandan sun samu bayanai cewa wasu da ake
zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare hanyar Assakio-
Sabon Gida.

Ramhan Nansel, ya ce an kama wani da ake zargin dan
bindiga ne a yankin Assakio, rike da wata bindiga mai dauke
da harsashi bakwai a cikin ta.

Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Maiyaki Baba, ya yaba wa
jami’an bisa wannan nasara da su ka samu, sannan ya bukaci
su kara zage damtse wajen fatattakar ‘yan ta’adda a fadin
jihar.