Home Labaru Mataimakin Shugaban Apc Ya Cire Musulmai a Yan Takarar Shugabancin Majalisa

Mataimakin Shugaban Apc Ya Cire Musulmai a Yan Takarar Shugabancin Majalisa

1
0

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso
yamma Salihu Lukman, ya ce bai dace Musulmi ya nemi
kujerar shugaban majalisar dattawa ba.

Rahotanni sun Ambato Salihu Lukman ya na cewa, duk musulmin da ya ke harin wannan kujerar ba ya ganin darajar kundin tsarin mulki.

Salihu Lukman ya yi wannan furucin ne, ganin cewa zababben shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima duk Musulmai ne.

Ya ce yunkurin tsaida wani Musulmi ya zama shugaba a majalisar tarayya zai janyo addinin Musulunci ya yi baba-kere a gwamnatin Nijeriya.