Home Labaru Mayakan Boko Haram Sun Kashe Mutum 10 a Yobe

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Mutum 10 a Yobe

26
0

Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton mayakan Boko
Haram ne, sun kashe mutane 10 a garin Buni Gari da ke
Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Alhamis da ta gabata, inda ‘yan ta’addan su ka kashe wani mutum mai suna Abba Sheti Gawi, lokacin da ya je saran itace a yankin Gangatilo.

Wata Majiya ta ce, abokai da ‘yan’uwan ​​mamacin sun hada kai domin bincike a yankin, amma ‘yan ta’addan su ka yi musu kwanton-bauna.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP Dungus Abdulkareem ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce mutane tara ne ‘yan ta’addan su ka kashe.

Leave a Reply