Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kashe ’Yan Bindiga 2, Sun Raunata Da Dama A...

‘Yan Sanda Sun Kashe ’Yan Bindiga 2, Sun Raunata Da Dama A Katsina

33
0

Akalla ‘yan bindiga biyu ne su ka gamu da ajalin su, yayin da
wasu da dama su ka tsere da raunuka bayan wata arangama da
jami’an ‘yan sanda a Jihar Katsina.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ‘yan sandan su ka yi musayar wuta da ‘yan bindigar a gidan wani Sarkin Fulanin kauyen Danmarke, wanda ke gundumar Dagwarwa a Karamar Hukumar Kurfi.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun yi ta harbe-harbe da bindigogi kirar AK 47 a kauyen, lokacin da jami’an tsaro su ka isa kauyen bayan sun amsa kiran neman taimako.

Bayanai sun ce, mai magana da yawun ‘yan sandan reshen yankin Kurfi ne ya jagoranci artabun da aka yi da ‘yan bindigar kuma aka samu nasarar fatattakar su.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar CSP Gambo Isah, ya ce rundunar ta gano cewa wasu da dama daga cikin yan ta’addan sun tsere da raunin bindiga, sannan su na gudanar da kwarya- kwaryan bincike domin gano inda wadanda su ka samu rauni su ka shiga.

Leave a Reply