Home Muryar 'Yanci ‘Yan Daba Sun Sace Akwatun Zabe Yayin Zaben Cike Gurbi a Jihar...

‘Yan Daba Sun Sace Akwatun Zabe Yayin Zaben Cike Gurbi a Jihar Imo

32
0

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da kai harin kwace
Akwatin zaɓe yayin da ake gudanar da zaben cike gurbi a
jihar Imo.

Rahotanni sun ce, ‘yan daba sun kutsa kai tare da sace Akwatin zaɓe a ƙaramar hukumar Isu ta jihar Imo.

Bayanai sun nuna cewa, ana zargin ‘yan daban sun samu taimakon jami’an tsaron da aka tura wurin, har su ka samu damar kutsa kai cikin sauki su ka yi awon gaba da Akwatin zaɓe.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan daban sun shiga rumfar zaben ne da misalin ƙarfe 9:19 na safe, duk kuwa da tulin jami’an tsaron da aka tura domin tsare kayan zaɓe a mazaɓar.

Leave a Reply