Home Labaru Jirgin Yakin Najeriya Ya Yi Wa Yara Luguden Wuta

Jirgin Yakin Najeriya Ya Yi Wa Yara Luguden Wuta

760
0

Akalla mutane 17 ne suka mutu bayan jirgin yakin Nijeriya ya bude masu jefa wuta bisa kuskure a jihar Borno.

Harin jirgin sojin ya hallaka mata da kananan yara da ke wasa a karkashin wata bishiya yakin Sakotoku da ke Karamar Hukumar Damboa.

Jirgin yakin ya jefa wa mutanen bamabamai ne bayan rundunar sojin sama ta Nijeriya ta samu labarin taruwar mayakan kungiyar Boko Haram a yankin, lamarin da ya sa aka shirya musu luguden wuta.

Sai dai maimakon kai harin a yankin Korongilum inda ‘yan ta’addan suka taro, sai jirin ya yi kuskuren bude wuta a Sakotoku mai makwabtaka da Korongilum da kusan nisan kilomita 12.

Ana kuma zargin yiwuwar an samu gibi a musayar bayanai tsakanin sojin sama da na kasa, a lokacin da jiragen yakin sojin sama suka jefa bamabamai a kauyen Sakotoku, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 17 da raunata wasu da dama.

An garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibitin Runduna ta 25 da ke Damboa, sannan wadanda ke cikin mawuyacin hali an mika su zuwa Maiduguri.