Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Bindige Jami’An ‘Yan Sanda Biyu A Jihar Rivers

‘Yan Bindiga Sun Bindige Jami’An ‘Yan Sanda Biyu A Jihar Rivers

172
0

‘Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu da ke aiki a ofishin rundunar na Mile One da ke birnin Port Harcourt na jihar Rivers.

Wata majiya ta ce, an bindige jami’an tsaron ne yayin da su ke aikin binciken ababen hawa a unguwar Okija da ke yankin.

Majiyar ta ce, ‘yan bindigar sun yi wa ‘yan sandan kwaton-bauna ne, inda bayan sun bude masu wauta su ka mutu nan take.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar SP Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply