Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Gidajen Malaman Makaranta A Abuja

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Gidajen Malaman Makaranta A Abuja

93
0

‘Yan bindiga sun kai hari gidajen malaman wata makarantar sakandare da ke yankin Yebu a karamar hukumar Kwali a Abuja, inda su ka sace mataimakin shugaban makarantar Mohammed Nuhu.

Wani malami da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce ‘yan bindigar, dauke da manyan makamai ne su ka kai hari gidajen malaman makarantar.

Ya ce wasu daga cikin ‘yan bindigar sun mamaye gidajen malaman, yayin da sauran tawagar su ka haura katanga zuwa cikin harabar, inda daga nan ne su ka fasa gidan sa sannan su ka yi awon gaba da shi.

Malamin, ya ce maharan sun daure jami’in tsaron gidajen kafin su bude kofar gidan, har ta kai da wasu malaman da ke zama a cikin gidajen sun gaza fita saboda yadda ake harbi da bindiga babu kakkautawa.

Shugaban kungiyar malamai ta Nijeriya reshen birnin tarayya Abuja Comrade Stephen Knabayi, ya tabbatar da sace mataimakin shugaban makarantar, inda ya ce lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan an sace babban limamin masallacin Juma’a na Yabgoji.