Home Labaru ‘Yan Takarar Gwamna 9 Sun Yi Kira A Saki Nnamdi Kanu

‘Yan Takarar Gwamna 9 Sun Yi Kira A Saki Nnamdi Kanu

146
0

‘Yan takarar kujerar gwamnan jihar Anambra 9, sun bukaci a saki shugaban kungiyar ‘yan a-waren Biafra Nnamdi Kanu.

Wannan dai ya na zuwa ne, yayin da su ka yi kira ga gwamnatin tarayya ta janye sojoji daga yankin kudu maso gabas a kokarin dakile fargabar da ke yankin.

‘Yan takarar sun bayyana matsayin su ne, a cikin wata sanarwar hadin gwiwa dauke da sa hannun Ben Etiaba na jam’iyyar AA, da Charles Soludo na jam’iyyar APGA da Obinna Uzoh na jam’iyyar SDP da kuma Akachukwu Nwankpo na jam’iyyar ADC.

Sun kuma nuna jin dadin su a kan damuwar da majalisar sarakunan gargajiya ta kudu maso gabas da wakilan Fastocin al’ummomin Igbo su ka nuna game da fargabar da ke tattare da tashe-tashen hankula a yankin.

Leave a Reply