Home Labaru Yaki Da Rashawa: Zan Iya Bankado Ma Buhari Naira Tiriliyan 3 –...

Yaki Da Rashawa: Zan Iya Bankado Ma Buhari Naira Tiriliyan 3 – Maina

341
0

Tsohon shugaban hukumar fasho ta kasa Abdulrashid Maina ya zargi shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da kuma tsohon shugaban hukumar Ibrahim Lamorde da laifin wawure naira Tiriliyan 1 da billiyan 63 da kuma gidaje 222 daya kwato.
Maina, ya bayyana hakan ne a lokacin da ake gabatar da wani shiri a gidan rediyon Human Right dake Abuja, inda ya ce saboda haka ne hukumar EFCC ta matsa masa take naman wulakan tashi.
Maina, ya zargi Ibrahim Magu da Ibrahim Lamorde da kwashe kudaden tare da raba gidajen ga wasu manyan mutane, domin haka ba za su iya bada cikakken bayanin gaskiya game da kudaden ba.
Ya kara da cewa ko a yanzu zai iya taimaka wa gwamnatin Buhari wajen bankado kimanin naira Tiriliyan 3 da aka sace, amma wasu shafaffu da mai kuma yan gaban goshi sun hanashi haduwa da Buhari gaba da gaba.

Leave a Reply