Home Labaru Rikicin Sarautar Kano: Ganduje Ya Ce Na Akan Bakarsa

Rikicin Sarautar Kano: Ganduje Ya Ce Na Akan Bakarsa

318
0
An ba wa jami'an tsaro umurnin tabbatar da ganin jama'a sun bi dokar hana fitar a fadin jihar.
Dokar hana zirga-zirgar za ta fara aiki daga ranar Alhamis har na tsawon kwana bakwai a karon farko.

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ba za ta taba sauka daga matsayinta ba kan dokar sabbin masarautun da ta kirkiro guda hudu.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya mika sandar Girma ga sabbin sarakunan duk da umarnin da wata kotu ta bayar na dakatar da taron bikin.
Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi Sunusi, ya isa filin jirgin saman na Malam Aminu Kano a yammacin jiya Lahadi bayan ya dawo daga aikin Umra a kasar Saudiya, inda masoyansa suka yi masa tarba ta musamman cikin farin ciki, yayinda suka yi masa rakiya zuwa fadar sa.
Da dama daga cikin magoya bayansa suka yi ado da riguna da huluna dauke da sunan basaraken, yayin da wasu kuma suke kade-kade da raye-rayen maraba.
Rahotanni na cewa, Sarkin bai yi wani jawabi ba bayan isowarsa Najeriya daga Saudiya.

Leave a Reply