Home Labaru Kiwon Lafiya Bincike: Ciwon Zuciya Na Kara Yawan Mutuwar Mutane A Duniya

Bincike: Ciwon Zuciya Na Kara Yawan Mutuwar Mutane A Duniya

689
0

Wani sabon bincike ya ce mace-macen da ake samu sakamakon cutukan zuciya da hanyoyin gudanar jini na k’aruwa a tsakanin mafi yawan al’umma karon farko a cikin shekara 50.
Gidauniyar kula da lafiyar Zuciya ta Burtaniya ta ce cutuka irinsu ciwon suga da hawan jini sun ba da gudunmawa wajen haddasa karuwar mace-macen.
Kafin ‘yan shekarun nan, mace-macen da ake samu sakamakon ciwon zuciya da toshewar magudanan jini sun ragu da kashi 75 cikin 100 tun daga 1971.
Sai dai wannan ci gaba a yanzu ya fuskanci koma-baya a cewar Gidauniyar Zuciya ta Duniya, inda mutane fiye da dubu 42 ‘yan kasa da shekara 75 ke mutuwa daga wannan cutuka a shekara ta 2017 karin kashi uku cikin 100 daga shekara ta 2014.
Sabubba irinsu tarin maik’o da hawan jini da taiba duka suna taka rawa a cewar gidauniyar.
Ta ma kara da cewa miliyoyin mutane ne ba su ma san suna da wadannan larurori ba.
Gidauniyar Zuciya ta Burtaniya ta ce wadannan sabbin alkaluma, ababen damuwa ne matuka, don haka ta bukaci k’ara zuba kudi cikin ayyukan bincike.

Leave a Reply