Home Labaru Tashin Hankali: Mutane Biyar Sun Mutu, An Kona Gidaje 12 A Jihar...

Tashin Hankali: Mutane Biyar Sun Mutu, An Kona Gidaje 12 A Jihar Filato

359
0
Pic 41. Traders at scene of fire incidence at Abubakar Gumi Central Market in Kaduna on Wednesday (20/2/2019) 01539/20/2/2019/Ibrahim Bashir/ICE/NAN

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ta ce mutane biyar sun mutu, an kuma kona gidaje 12 a wani rikici da ya barke ranar Lahadin da ta gabata a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Tyopev Terna ya bayyana wa manema labarai cewa, rikicin ya auku ne a garuruwar Dutse Uku da Unguwar Damisa da ke karamar hukumar Jos ta arewa sakamakon tsintar gawar wani matashi mai suna Enoch Monday.

Terna ya ce kafin rikicin ya barke, wani mazaunin kauyen Tina mai suna Sarki Arum ya kai kara ofishin su cewa sun tsinci gawar matashin, lamarin da ya sa su ka gaggauta dauke gawar amma kafin su ankara labarin mutuwar Monday ta karade kauyukan, inda matasan kauyukan su ka fara zanga-zanga.

Ya ce rikicin ya yi sanadiyyar rayukan mutane biyar, sannan an kona gidajen 12 sakamakon zanga-zangar da matasan su ka yi.

A karshe ya ce rundunar, tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro sun tsaida wannan rikici, kuma an samar da tsaro a wadannan unguwanni.

Leave a Reply