Home Labaru Yaki Da Rashawa: NNPC Ta Yi Barazanar Sallamar Ma’aikata 1,0506 -Kyari

Yaki Da Rashawa: NNPC Ta Yi Barazanar Sallamar Ma’aikata 1,0506 -Kyari

463
0

Kamfanin matatar mai ta Najeriya NNPC, ta yi barazanar sallamar ma’aikatan kamfanonin mai 21 dake Najeriya kan rashin gaskiya da cin hanci da rashawa.

Mele Kolo Kyari, Shugaban Kamfanin matatar mai

Shugaban kamfanin Mele Kolo Kyari, ya tabbatar da haka a yayinda yake jawabi a liyafar da aka shiryawa ma’aikatan, inda ya ce akwai kulle-kulle da boye-boye da cuwa-cuwan da ma’aikatan Depo-Depo suka shahara da shi.

Ya jaddadawa manajojin kamfanin da ma’aikatan cewa duk wanda aka kama da rashawa zai rasa aikinsa ba tare da bata lokaci ba.

Mele Kyari, ya yi kira ga ma’aikatan su kamanta gaskiya wajen ayyukansu na yau da kullum saboda cimma manufan ma’aikatar.

Shi ma daraktan yada labarai na kamfanin Ndu Ughamadu, ya ce Shugaban kamfanin ba zai lamunci cuwa-cuwan da aka saba yi a baya ba, duk ma’aikacin da aka kama da rashawa zai fita daga ma’aikatar ba tare da bata lokaci ba.

Kyari, ya janyo hankalin ma’aikatan su kai karan duk wani babban da suke ganin yana ha’inci, kuma kamfanin NNPC zai karrama duk ma’aikacin da ya gudanar da aikinsa da kyau.