Home Labaru Ci Rani: Majalisar Legas Ta Yi Alla-Wadai Da Sakin ‘Yan Arewa 123...

Ci Rani: Majalisar Legas Ta Yi Alla-Wadai Da Sakin ‘Yan Arewa 123 Da Aka Kama

570
0

Majalisar dokokin jihar Legas ta yi Alla-wadai da sakin ‘yan asalin jihar Jigawa 123 da hukumar tabbatar da tsari a jihar ta yi.

Sanai Agunbiade, Shugaban masu rinjaye a majalisar Legas

Shugaban masu rinjaye a majalisar Sanai Agunbiade, ne ya taso da maganar ya yin zaman majalisar, inda ya ce babu wanda ya san menene nufin mutanen da suka shigo jihar da babura masu yawa, wanda hakan ke barazana ga tsaro a jihar.

‘Yan majalisar sun koka akan yadda Hausawa ke tururuwar shiga garin Legas, da babura ko motoci cike da shanu, tare da yin kira ga kwamishinan ‘yan sandan jihar akan ya tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar mutanen jihar Legas.

Kazalika, majalisar ta yi kira ga majalisun tarayya su sake yin duba akan kudirin bukatar kirkirar ‘yan sandan jihohi.

Wani dan majalisar mai wakiltar mazabar Amuwo ta daya Macauley Mojisola, ya ce akwai bukatar gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu, ya sanar da sauran gwamnoni akan su sanar da mutanensu bukatar yin biyayya ga dokokin jihar Legas.

Shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, ya ce ya na goyon bayan abinda ‘yan majalisar suka fada tare da bayyana cewa kasafin kudin jihar Legas ba zai isa adadin mutanen dake shigo musu ba.