Home Labaru Tsaro: Sojojin Sun Kwato Dabbobi 134 Daga Hannun Barayi A Kaduna

Tsaro: Sojojin Sun Kwato Dabbobi 134 Daga Hannun Barayi A Kaduna

969
0

Kwamandan rundunar Sojin Najeriya ta 1, Birgdeiya Jimmy Akpor, ya mika wa jami’an gwamnatin jihar Kaduna shanu 134 da suka kwato daga hannun ‘yan bindiga dake satar shanu a Kaduna.

Kwamandan rundunar Sojin Najeriya ta 1, Birgdeiya Jimmy Akpor

Birgediyan Jimmy, ya mika wadannan dabbobi ga wakilin gwamnatin Kaduna, kuma shugaban Operation Yaki na jahar, Murtala Abbas, a kauyen Kakau dake karamar hukumar Chikun.

Shanu 120 da kuma awaki 14, wadanda dukkaninsu an kwato su ne daga hannun wani kasurgumin dan bindiga mai suna Aminu Mallam, wanda ake yi wa inkiya da Baderi, wanda Sojoji suka kama shi a kauyen sabon Gayan.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban Operation Yaki Murtala Abbas, ya ce za su mika dabbobin ga sashin binciken manyan laifuka na hukumar ‘Yan sandan Najeriya domin gudanar da cikakken bincike kafin su mika ma masu dabbobin hakkokin su.

Ya ce za a binciko masu dabbobin, sannan sai an tabbatar da gaskiyar mutum kafin abashi dabbobinsa, kuma za a bukaci lokacin da aka sace dabbobin da adadinsu da dai sauran bayanai, kafin su bari mutum ya yi ido hudu da dabbobin.