Home Labaru Yaki Da Rashawa: An Gano Wasu Kayan Cuwa-Cuwa Da Ake Zargin Wasu...

Yaki Da Rashawa: An Gano Wasu Kayan Cuwa-Cuwa Da Ake Zargin Wasu Manyan ‘Yan Siyasa

260
0

Hukumar yaki da rashawa ICPC, da Kungiyar Bibiyar Ayyukan Mazabu na ‘yan Majalisa CPTG, sun gano wasu kayayaki da aka ware domin amfanin talakawa a wasu yankunan jihohin Akwa Ibom da Bauchi.

 Kayayakin da aka gano sun hada da na’urar tace jini da janareta da wasu kayayakin asibiti, a wani gida da aka yi ikirarin na Sanata Godswill Akpabio ne, yayin da aka gano wasu taraktocin noma guda shida da ya dace a ba manoma a kananan hukumomi shida na mazabar Bauchi Ta Tsakiya da Sanata Isa Hamman Misau ke wakilta.

Isa Hamman Misau ya shaida wa jami’an ICPC cewa, taraktocin su na ne ajiye a kauyen Yuli, amma da tawagar Kungiyar Bibiyar Ayyukan Mazabu ta je kauyen kuma babu su babu dalilin su.

Daga bisani bincike ya nuna cewa, an yi gaugawar kai taraktocin helkwatar karamar hukumar Ganjuwa, inda aka lura cewa duk sun fara lalacewa saboda amfani da su da ake yi wasu daga cikin su na zubar da bakin mai.

Tuni dai hukumar ICPC ta kwace kayayakin, ta kuma damka su a hannun shugaban karamar hukumar Ganjuwa kafin lokacin da za a kammala bincike.