Home Labaru Zaman Lafiya: Farfesa Yemi Osinbajo Ya Jinjina Wa Jihohin Kano Da Lagos

Zaman Lafiya: Farfesa Yemi Osinbajo Ya Jinjina Wa Jihohin Kano Da Lagos

455
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Obasanjo, ya yi wa jihohin Lagos da Kano muhimmiyar jinjina, inda ya ce jihohin biyu sun zama abin koyi ta fuskar rungumar dukkan Nijeriya a biranen su, lamarin da ya ce ya na kara janyo masu ci-gaba tare da kara inganta zaman lafiya a fadin kasar nan.

Ya ce hadakar kabilu daban-daban kan iya haifar da zaman lafiya da kulluwar zumunci ko kuma haddasa rikici, kamar yadda ta sha faruwa a wurare daban-daban a fadin duniya.

Farfesa Yemi Obasanjo,

Osinbajo ya cigaba da cewa, yawan kabilu daban-daban a kasa daya ba matsala ba ne, ana samun matsala ne ta yadda kabilun su ka mu’amalanci junan su, don haka samun nasara a matsayin kasa mai kabilu da yawa ya dogara ne a kan yadda jama’a su ka jibanci lamuran juna.

Da ya ke bada misalin jihohin da su ka yi amfani da bambacin kabila wajen sama wa kan su ci-gaba, Osinbajo ya ce ci-gaba da habakar tattalin arzikin jihohin Kano da Legas ya na da alaka da rungumar kabilu daban-daban da su ka yi a biranen su.

Farfesan, ya sake yaba wa jihohin bisa kokarin sa na bada mukaman siyasa ga kabilun da ba ‘yan asalin jihar su ba, tare da cewa hakan ya haifar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin asalin mutanen jihohin da bakin da su ke zaune a biranen.