Tsohon Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnati ta kafa kwamitin bincike domin tabbatar da zargin cewa rundunar sojin Nijeriya ta binne sojoji sama da 1,000 da su ka mutu lokacin yaki da kungiyar Boko Haram cikin sirri a Maiduguri.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Atiku Abubakar, ta bukaci a kafa kwamitin shari’a domin gudanar da bincike, sakamakon rahoton da Jaridar Wall Street Journal ta wallafa.
Sai dai ma’aikatar tsaron Nijeriya ta hannun kakakin ta Kanar Onyeama Nwachukwu ta yi watsi da zargin, wanda ta danganta da labarin kanzon-kurege.
Ma’aikatar tsaron ta ce, ta na gudanar da jana’izar duk sojojin da ta rasa kamar yadda dokokin Nijeriya su ka tsara a bayyane, don haka babu gaskiya a cikin labarin cewa rundunar sojin ta na da makabarta ta sirri.
Jaridar Wall Street Journal da ke kasar Amurka ta wallafa cewa, rundunar sojin ta binne dakaru dubu ko sama da haka da su ka kwanta dama a yaki da Boko Haram a cikin sirri, yayin da shugaba Buhari ya yi shirin kai ziyara jihar Borno a watan Nuwamba.